Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Jaridar yahudawa "Yedioth Aharonoth" a yau Juma'a ta ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta daina ɗaukar kwance damarar ƙungiyar Hamas a matsayin sharaɗin fara sake gina zirin Gaza da kuma ajiye wata runduna ta duniya a cikinta.
Yedioth ta yi iƙirarin cewa bayan aiwatar da matakin farko na wannan yarjejeniya, Amurka, saboda tasirin matsayin Qatar da Turkiyya da kuma bukatunta na yanki, ta ɗauki hanya mai sassauƙa game da Hamas.
Wannan jaridar ta kuma yi iƙirarin cewa Isra'ila ta dage kan kwance damarar Hamas, kuma wannan lamari ne ya haifar da faɗaɗa sabani tsakanin bangarorin biyu game da makomar wannan yanki. Duk da cewa masana suna ganin duk wani sabani tsakanin Isra'ila da Amurka game da al'amuran yanki a matsayin na zahiri ne kawai amma ta ciki na ciki.
Bisa ga wannan rahoto, Amurka a yanzu tana neman cimma yarjejeniya wadda "ta haɗa da kwance damarar Hamas a wani bangare, ta yadda za a kawar da manyan makamai, yayin da za’a bar wannan ƙungiya ta riƙe kananan makamai; amma tattaunawar na ci gaba da fuskantar matsala saboda rashin samun ma'anar da aka amince da ita game da manyan makaman.
Kwance damarar Hamas na ɗaya daga cikin muhimman batutuwa na shirin da Donald Trump, shugaban Amurka, ya yi iƙirarin don kawo ƙarshen yaƙin Gaza da fara sake gina wannan yanki. Matakin farko na wannan yarijeniya, ya haɗa da mayar da ragowar fursunonin Isra'ila da 'yantar da fursunonin Falasdinu 250 da fararen hula 1,700 daga zirin Gaza, yayin da kwance damarar wannan ƙungiya ke cikin mataki na gaba na wannan shiri.
Wata cibiyar Amurka da ake kira "Majalisar Zaman Lafiya ta Gaza" ta yi iƙirarin cewa ba za a fara sake gina Gaza ba tare da kwance damarar Hamas ba. Wannan majalisa wadda a baya aka bayyana cewa Trump ya karbi dala biliyan 17 daga gare ta kuma ya ajiye su a asusun Isra'ila, ta ce sake gina Gaza na buƙatar fiye da dala biliyan 30.
Sake Gina Gaza Ba Ya Dogara Da Kwance Damarar Gaba Daya
Yedioth ta ce Washington ta yanke shawarar cewa duk da rashin cimma burin kwance damarar, za a fara mataki na biyu na shirin Trump, wanda ya haɗa da fara sake gina yankunan da Isra'ila ta mamaye a cikin zirin Gaza a hankali, janye sojojin Isra'ila daga cikinsu, da kuma ajiye wata runduna ta duniya don tafiyar da waɗannan yankuna.
Shafin Isra'ila "Walla" shi ma ya ba da rahoton fara shirya wata runduna ta duniya da kayan aikin soji don "ɗaukar alhakin tabbatar da tsaro a wasu sassan zirin Gaza." Walla ta kuma ce wannan rukunin tun jiya, "ya karɓi motoci da dama, ciki har da motocin sulke."
Gidan rediyo da talabijin na Isra'ila a wannan fanni ya ruwaito cewa Masar ta sake gabatar da wata shawara, wadda bisa gare ta, Hamas, a maimakon kwance damarar gaba daya, za ta ajiye makamanta a wurin Cairo a matsayin amana.
Wannan gidan ya nakalto daga wata majiya ta Masar cewa Alkahira tana matsa wa Hamas don ta karɓi wannan shawara a matsayin madadin kwance damarar don a kai ga zuwa mataki na biyu na shirin Trump na kawo ƙarshen yaƙi a Gaza. Wannan majiya ta kuma ce Hamas ta ƙi wannan shawara da ƙarfi, kuma ta jaddada wajabcin kiyaye makamanta.
…………………………….
Your Comment